Jummaʼa 11 Yuli 2025 - 22:44
Ya Kamata Ƙungiyoyin Ƙasa da Ƙasa Su Yi Allah-Wadai da Kisan, a Hukunta Waɗanda Suka Aikata Shi da Masu Mara Musu Baya

Hauza/ Shugaban Makarantun Hauza ya bayyana cewa yana kira ga dukkan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, musamman Majalisar Ɗinkin Duniya, Majalisar Kare Haƙƙin Ɗan’adam, Babban Kwamishinan Kare Haƙƙin Ɗan’adam, Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci da Ƙungiyar Malaman Musulmi, da su yi Allah-wadai nan take da kisan da aka yi wa malaman Shi’a a Syria, tare da hukunta waɗanda suka aikata laifin kai tsaye da masu mara musu baya a yankin da kuma na ƙasa da ƙasa.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A’arafi, shugaban Makarantun Hauza na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya fitar da sanarwa domin yin Allah-wadai da kisan malaman Shi’a a Syria, tare da neman ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su ɗauki matakin gaggawa.

Ga fassarar cikakkiyar sanarwar:

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Cikin matuƙar baƙin ciki da alhini, mun sake ganin yadda hannayen ta’addancin masu tsattsauran ra’ayi da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi masu alaƙa da tsarin mamayar duniya da yahudawan sahyoniya suka aikata wani mummunan laifi, inda suka yi sanadin shahadar wasu manyan malaman Shi’a masu daraja da ilimi a ƙasar Syria.

Wannan babban bala’i ba wai kawai keta dukkan ƙa’idojin ɗan’adam, haƙƙoƙin bil’adama da koyarwar addini ba ne, har ila yau, yana nuna ci gaba da wani shiri mai haɗari na amfani da bambancin addini wajen haddasa tashin hankali da rarrabuwar kai a yankin.

Yayin da muke yin Allah-wadai da wannan mummunan laifi da kakkausar murya, muna bayyana cewa shirun ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da hukumomin da ke ikirarin kare haƙƙin ɗan’adam a kan irin waɗannan munanan laifuka da ake ta maimaitawa, yana taimakawa wajen yaɗuwar tashin hankali, ƙiyayya tsakanin mazhabobi, tare da zama barazana ga tsaron ƙasa da ƙasa.

Ina kira ga dukkan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, musamman Majalisar Ɗinkin Duniya, Majalisar Kare Haƙƙin Ɗan’adam, Babban Kwamishinan Kare Haƙƙin Ɗan’adam, Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci da Ƙungiyar Malaman Musulmi, da su ɗauki matakai kamar haka:

1. Su yi Allah-wadai nan take da waɗannan laifuka, tare da hukunta waɗanda suka aikata su kai tsaye da masu mara musu baya a yankin da kuma na ƙasa da ƙasa.

2. Su kafa wata tawaga mai zaman kanta domin binciken gaskiya, tare da gaggauta gano waɗanda suka aikata waɗannan laifuka da tattara bayanan da za su tabbatar da hare-haren da aka kai kan malaman addini da ƙananan ƙungiyoyin addini a Syria.

3. Su yi amfani da damar da dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada, ciki har da dokokin kare haƙƙin ɗan’adam, dokokin jin ƙai a lokacin yaƙi da ƙa’idojin tabbatar da adalci a shari’ar manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa, domin gurfanar da waɗanda suka bayar da umarni da waɗanda suka aikata waɗannan laifuka a gaban shari’a, tare da hukunta su.

Malaman addini su ne masu ɗauke da ilimi, hikima da zaman lafiya. Kai musu hari yana nufin kai hari kan tushen wayewar ɗan’adam da kuma gadon ilimi da al’adu na bai ɗaya da ɗan’adam ya mallaka.

A ƙarshe, yayin da muke bayyana ta’aziyyarmu ga iyalan waɗannan shahidai da aka zalunta, al’ummar Syria da gwamnatinta, da duk masu son gaskiya da adalci, muna jaddada cewa Makarantun Hauza na duniyar Musulunci za su ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da al’ummomin yankin da ke fafutukar kare haƙƙinsu, wajen kare gaskiya, haɗin kan al’ummar Musulunci da kuma yaƙi da ta’addanci mai tsari.

وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنْقَلَبٍ يَنْقَلِبُونَ

"Da sannu waɗanda suka yi zalunci za su sani irin makomar da za su koma." (Suratus Shu’ara: Aya ta 227).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha